logo

HAUSA

Kasashen BRICS sun lashi takobin zurfafa hadin gwiwa kan harkokin kudi

2022-06-07 13:10:19 CMG Hausa

 

Ministocin kudin da gwamnonin manyan bankunan kasashen kungiyar BRICS, sun fidda wata sanarwar hadin gwiwa yayin taron da suka yi ta kafar bidiyo, inda suka cimma matsaya kan zurfafa hadin gwiwarsu a bangaren harkokin kudi da karfafa hadin gwiwa kan manufofin bunkasa tattalin arziki.

Taron na jiya, wanda ya gudana karkashin jagorancin gwamnan babban bankin Sin, Yi Gang da ministan kudin kasar Liu Kun, ya tattauna kan batutuwan da suka shafi inganta tsarin tallafawa da tunkarar matsalolin kudi na kungiyar da hadin gwiwar tallafawa manyan kamfanoni sauyawa zuwa amfani da makamashi mai tsafta da sauransu.

Yayin taron, Yi Gang, ya yabawa kokarin da dukkan kasashen BRICS suke yi na cimma nasarori a hadin gwiwarsu kan harkokin kudi.

Taron ya kuma yi kira ga kasashen duniya su kyautata hadin gwiwa, yana mai jaddada wajibcin karfafa manufofin kudi wajen ingiza fitar da tattalin arzikin duniya daga matsalar da yake ciki, tare da tsara shiri mai karfi da dorewa da kuma daidaito, wanda zai farfado da shi bayan kawo karshen annobar COVID-19. (Fa’iza Mustapha)