logo

HAUSA

Tennessee, Amurka: mutane 3 sun mutu a harbe-harbe yayin da wasu 14 suka jikkata

2022-06-06 14:40:23 CMG HAUSA

 

Da sanyin safiyar ranar 5 ga wata ne aka yi harbe-harbe a kusa da wani gidan shakatawa a birnin Chattanooga dake jihar Tennessee ta kasar Amurka, inda mutane 3 suka rasa rayukansu, yayin da wasu 14 suka jikkata.

A daren ranar 4 ga wata kuma, a kalla mutane 3 sun mutu a harbe-harbe na daban da aka yi a birnin Philadelphia da ke jihar Pennsylvania ta kasar, yayin da wasu 11 suka jikkata.

Kwanan baya, an yi ta samun harbe-harbe a Amurka daya bayan daya. Al’umma sun sake yin muhawara kan batun nuna karfin tuwo ta hanyar amfani da bindiga, da tabbatar da tsaro a makarantu, da dai sauransu. Masharhanta da dama suna ganin cewa, yin amfani da bindiga fiye da kima, da yadda masu cinikin bindiga suka kara azama kan cinikinsu, da kuma gazawar mahukunta, su ne dalilan da suka sanya irin wannan abin tausayi ya rika abkuwa a Amurka.

Bisa alkaluman da cibiyar “bayanan batutuwan nuna karfin tuwo ta hanyar amfani da bindiga” ta Amurka ta gabatar, an ce, a bana akwai harbe-harbe fiye da 240 a Amurka, inda mutane a kalla 4 suka mutu ko jikkata. Haka kuma, mutane fiye da dubu 18 sun rasa rayukansu sakamakon batutuwan nuna karfin tuwo ta hanyar amfani da bindiga cikin watanni fiye da 5 a Amurka. (Tasallah Yuan)