logo

HAUSA

Shugabar sashen lura da halittu ta MDD ta yaba nasarorin da Sin ta samu a fannin kare muhalli

2022-06-06 10:32:09 CMG Hausa

Elizabeth Maruma Mrema, babbar sakatariyar sashen kula da nau’ikan halittu ta MDD ta ce, kasar Sin ta cimma muhimman sakamako masu karfafa gwiwa a fannonin yaki da matsalar sauyin yanayi, da kandagarkin bacewar nau’in halittu, da rage iska mai gurbata muhalli.

Mrema ta yi wannan tsokaci ne a lokacin bikin ranar kare muhalli ta kasar Sin ta shekarar 2022, inda ta bayyana hakan a jawabin da ta gabatar ta kafar bidiyo. Taken bikin na bana shi ne, “mu yi aiki tare don gina kyakkyawar duniya mai tsafta," bikin wanda aka gudanar a Shenyang, babban birnin lardin Liaoning dake shiyyar arewa maso gabashin kasar Sin.

Mrema ta bayyana cewa, kasar Sin ta yi aiki tukuru, tare da bayar da gagarumar gudunmawa ga kokarin da duniya ke yi wajen magance matsalolin dake shafar muhalli, da daga matsayin aikin gina cigaba mai dorewa, da kuma gina makomar al’umma don kyautata rayuwar dukkan bil adama a duniya.

Bugu da kari, ta kuma yabawa matakan da kasar Sin ke dauka wajen kiyaye nau’ikan halittu, matakan da suka hada da kafa lambunan shan iska na kasa, da kuma shata dokokin dake shafar kiyaye muhallin halittu. (Ahmad)