logo

HAUSA

Wang Yi zai halarci taron ministocin harkokin waje karo na 3 na "Sin da kasashen tsakiyar Asiya 5"

2022-06-06 17:40:35 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya sanar yau Litinin cewa, bisa gayyatar da mataimakin firaministan kasar Kazakhstan, kuma ministan harkokin wajen kasar Mukhtar Tileuberdi ya yi masa, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, zai kai ziyara kasar Kazakhstan daga ranar 6 zuwa 9 ga wata, domin halartar taron ministocin harkokin waje karo na uku a tsakanin kasar Sin da kasashen tsakiyar Asiya guda biyar, da kuma ziyartar kasar ta Kazakhstan. (Mai fassara: Bilkisu Xin)