logo

HAUSA

Yan sama jannatin kumbon Shenzhou-14 sun shiga kumbon Tianzhou-4

2022-06-06 13:43:42 CMG Hausa

Ofishin kula da aikin zirga-zirgar sararin samaniya na kasar Sin ya ba da labari cewa, ‘yan sama jannatin kumbon dakon mutane na Shenzhou-14 wadanda suka shiga tashar binciken sararin samaniya sun bude kofar kumbon dakon kaya na Tianzhou-4 yau da misalin karfe 11 da minti 9, kuma sun shiga kumbon da karfe 12 da minti 19 lami lafiya bayan da suka bincika muhallin kumbon. Nan gaba ‘yan sama jannatin za su shiga kumbon dakon kaya na Tianzhou-3 domin jigilar kayayyakin da suke bukata. (Jamila)