logo

HAUSA

An samu masu bulaguron yawon bude ido kusan miliyan 80 a cikin gida a lokacin hutun Duanwu

2022-06-06 13:46:50 CMG Hausa

A yayin hutun kwanaki uku na bikin gargajiyar kasar Sin na hawa kwale-kwale wato Dragon Boat Festival, ya zuwa ranar Lahadi, an samu jimillar masu tafiye-tafiye don yawon shakatawa na cikin gida miliyan 79.61, kamar yadda ma’aikatar kula da al’adu da yawan bude ido ta kasar ta bayyana.

A cewar ma’aikatar, kudaden shigar da aka samu daga hada-hadar masu yawon bude ido na cikin gida a lokacin hutun ya kai CNY biliyan 25.82, kwatankwacin dala biliyan 3.85.

Ma’aikatar ta sanar cewa, kasuwar hada-hadar raya al’adu da yawon bude ido ta kasar Sin tana cikin yanayi mai kyau a lokacin hutun, kuma ta gudana bisa tsari yadda ya kamata.

Bikin gargaji na Dragon Boat, wanda aka fi sani da bikin Duanwu, wani lokacin hutu ne a bisa al’adar kasar Sin. Ana gudanar da bikin ne a ranar 5 ga watan 5 bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, inda bikin na bana ya fado a ranar Juma’a. (Ahmad)