logo

HAUSA

Putin: Moscow za ta dauki matakai da suka dace muddin Washington ta samar da makamai masu linzami ga Kiev

2022-06-06 12:55:40 CMG Hausa

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce Moscow za ta yanke hukunci mafi dacewa, kuma za ta afkawa sabbin wurare, matukar Washington ta kuskura ta shigar da makamai masu linzami dake cin nisan zango ga Kiev, Putin ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya gabatar ta gidan talabijin na Rossiya-1 na kasar a ranar Lahadi.

Mista Putin ya kara da cewa, saboda sojojin Ukraine suna da irin wadannan makamai, kuma aika irin wadannan makaman ga Kiev, babu abin da zai iya sauyawa, sai dai ya kara tsawaita yakin da ake gwabzawa.

A ranar Talata, shugaban kasar Amurka Joe Biden ya sanar da cewa, Amurka za ta samar da manyan makaman roka ga Ukraine bisa ga bukatar da Kiev ta nema.

A tattaunawar da ya yi ta wayar tarho da shugabannin kasashen Turai a ranar 28 ga watan Mayu, Putin ya bayyana cewa, samar da makaman zai kara tabarbarewar yanayin da ake ciki, kana zai kara ta’azzara yanayin bukatun jin kai a Ukraine. (Ahmad)