logo

HAUSA

Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna ga bikin kasa na ranar muhalli ta shekarar 2022

2022-06-05 17:50:29 CMG Hausa

Yau Lahadi, an shirya bikin ranar Muhalli ta kasa na shekarar 2022 a birnin Shenyang na lardin Liaoning dake arewa maso gabashin kasar Sin. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da wasikar taya murna domin nuna farin cikinsa kan gudanar da bikin.

A cikin wasikar, Xi Jinping ya yi nuni da cewa, muhallin halittu shi ne ginshikin rayuwa da ci gaban dan Adam, kuma kiyaye muhalli yadda ya kamata shi ne burin bai daya na jama'ar kasashe daban daban. A cewarsa, tun bayan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, kasar Sin ta dauki aikin raya al'adun halittu a matsayin wani muhimmin shiri mai alaka da samun dauwamammen ci gaban al'ummar kasar, tana kuma tsayawa kan ra’ayin “Kyakkyawan muhalli shi ne arzikinmu”. Bisa ga haka kuma, an gudanar da jerin sabbin ayyuka masu muhimmanci na dogon lokaci, kuma an dauki matakai masu muhimmanci wajen gina kyakkyawar kasar Sin, sannan an sa kaimi ga sauye-sauyen ayyukan kiyaye muhalli a dukkan fannoni da ba a taba ganin irinsa ba a tarihi.

Baya ga haka, Xi Jinping ya jaddada cewa, kamata ya yi daukacin jam'iyyar da ma kasar baki daya su ci gaba da azama kan kiyaye muhalli bisa manyan tsare-tsare, da kokarin sa kaimi ga samun ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al'umma ta hanyar kiyaye muhalli. Kana da daidaita ayyukan kula da gurbata muhalli, kiyaye muhalli da tinkarar sauyin yanayi, da kuma kokarin gina kyakkyawar kasar Sin inda bil’adama da yanayi za su kasance tare yadda ya kamata, don kara ba da gudummawa ga gina kyakkyawar duniya mai tsafta. (Mai fassara: Bilkisu Xin)