logo

HAUSA

‘Yan sama jannati dake cikin kumbon Shenzhou-14 sun shiga babban akwatin Tianhe

2022-06-05 21:38:57 CMG Hausa

Hukumar kula da ayyukan harba kumbuna masu dauke da mutane ta kasar Sin(CMSA) ta sanar a yau Lahadi cewa, da misalin karfe 8:50 na yammacin yau agogon Beijing, ‘Yan sama jannati dake cikin kumbon Shenzhou-14 , da suka hada da Chen Dong, Liu Yang da kuma Cai Xuzhe, sun shiga babban akwatin Tianhe, kamar yadda aka tsara.

Da misalin karfe 10:44 na safiyar yau bisa agogon Beijing, aka harba kumbon Shenzhou-14, wanda ya hadu da tashar sararin samaniya da ke da sassan da suka hada da babban akwatin Tianhe da kuma kumbon Tianzhou-3 da na Tianzhou 4 masu dakon kaya da misalin karfe 5:42 na yammacin yau Lahadi agogon Beijing, bayan ya gudanar da sauye-sauyen hanyarsa har sau shida ta hanyar sarrafa kansa.

Wannan aiki shi ne karo na 23, tun bayan da aka kaddamar da ayyukan harba kumbuna masu dauke da 'yan sama jannati na kasar Sin, shi ne kuma karo na 3 da aka gudanar da aikin a matakin tashar sararin samaniya.

Cikin watanni shida masu zuwa, ‘yan sama jannatin za su gudanar da wasu ayyukan da suka shafi kiyayewa da kula da dandalin tashar, da sarrafa hannayen mutum-mutumi, da fita daga akwatin, da ma wasu gwaje-gwajen kimiyya da fasahar sararin samaniya. (Ahmad)