logo

HAUSA

Antonio Guterres ya bukaci a bada fifiko kan hada-hada mai dorewa gabanin ranar muhalli ta duniya

2022-06-05 17:57:06 CMG Hausa

Babban sakataren MDD, Antonio Guterres, ya bukaci kamfanonin kasa da kasa da su bayar da fifiko wajen tabbatar da dorewa gabanin ranar muhalli ta duniya, wacce aka saba gudanarwar a ranar 5 ga watan Yunin kowace shekara.

Jami’in MDDr ya ce, “Muna bukatar abubuwa masu tarin yawa a wannan duniyar tamu domin tafiyar da rayuwarmu, wadanda ba masu dorewa ba ne," kuma lamarin ba kawai yana cutar da duniyar ba ne, har ma da halittun dake rayuwa cikinta.

Sama da mutane biliyan 3 ne matsalolin tabarbarewar muhallin halittu ya shafa a duniya.  Gurbacewar muhalli tana sanadiyyar mutuwar wuri na kusan mutane miliyan 9 a duk shekara a duniya, kuma sama da nau’ikan dabbobi da tsarrai miliyan 1 ne ke fuskantar barazanar bacewa daga doron kasa a duk shekara a duniya, wasu da dama kuma na faruwa ne a cikin gwamman shekaru, kamar yadda babban jami’in MDDr ya bayyana.

Ya kara da cewa, nan da shekarar 2050, sama da mutane miliyan 200 ne a duk shekara zasu fuskanci barazanar barin muhallansu sakamakon matsalolin sauyin yanayi.

Guterres ya bukaci gwamnatoci da su bada fifiko wajen daukar matakan tinkarar matsalolin sauyin yanayi, da kare muhalli, ta hanyar bullo da manufofin da zasu taimaka wajen tabbatar da ci gaba mai dorewa.

Sakatare janar din ya kuma zayyana wasu muhimman shawarwari game da yadda za a mayar da hankali wajen amfani da makamashin da ake iya sabuntawa.

Ranar muhalli ta duniya, ta kasance a matsayin wani muhimmin lokaci da MDD ke amfani da shi, wajen fadakar da duniya game da matakan da suka dace a dauka don kare muhalli. Taken ranar na wannan shekara shine, “Duniya daya tilo ce."(Ahmad)