logo

HAUSA

Bakaken fata da dama sun bar gwamnatin shugaba Biden, in ji wani rahoto

2022-06-03 16:32:10 CMG Hausa

Wani rahoton da kamfanin watsa labarai na Politico na Amurka ya fitar a ranar Alhamis, ya nuna yadda sama da bakaken fata 20, dake aiki a fadar White House ta Amurka, suka ajiye ayyukan su tun daga shekarar bara zuwa yanzu, a wani mataki da rahoton ya yiwa lakabi da "Blaxit," wato ficewar jami’ai daga gwamnatin Biden.

Duk da cewa wasu daga irin wadannan jami’ai, sun ajiye aikin su ne saboda burin ko dai karo karatu, ko tunkarar wasu ayyukan na ci gaba, rahoton ya ce wasun su sun bar aikin fadar shugaban na Amurka ne saboda rashin samun karsashin aiki, da karancin damammaki.

Wani jami’i da a yanzu haka ke aiki a fadar gwamnatin ta Amurka, ya ce gwamnatin mai ci, ta gayyato bakaken fata cikin ta, ba tare da kafa musu wani tsari na wanzar da ci gaban su, ko taimakawa samun nasarar su ba.

Shi kuwa wani tsohon jami’in fadar gwamnatin cewa ya yi, wasu daga cikin rukunin na bakaken fata da suka shiga gwamnatin Biden, ba su ji dadin tsarin ba, saboda rashin yanayin aiki mai dacewa da bakaken fata.   (Saminu)