logo

HAUSA

Fashewar gas ta jikkata a kalla mutane 20 a jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya

2022-06-03 19:59:25 CMG HAUSA

Rahotanni daga jihar Kano dake arewa maso yammacin Najeriya na cewa, wata fashewa mai nasaba da iskar gas da ta auku a jiya Alhamis, a wani gidan mai dake karamar hukumar Kumbotsa, ta jikkata a kalla mutane 20.

A cewar kakakin hukumar kashe gobara ta jihar Saminu Yusif, binciken farko farko ya nuna cewa, wata tukunyar gas da wani mai tuyar kifi dake kusa da gidan man ke amfani da ita ce ta yi bindiga, kuma nan take ta haifar da tashin gobara a gidan man.   (Saminu)