logo

HAUSA

Kalaman Xi Jinping Game Da Kishin Kasa

2022-06-03 15:52:32 CMG HAUSA

A bana yau Juma’a ce ranar da Sinawa ke murnar bikin Duanwu. An fara gudanar da wannan biki na musamman ne, domin tunawa da wani shahararren marubucin rubutattun wakoki mai kishin kasa mai suna Qu Yuan, wanda ya rayu a zamanin daular Zhanguo wato the Warring States Period a Turance wato tsakanin shekarar 475 zuwa 221 kafin haihuwar Annabi Isa A.S..

Qu, ya rubuta wakoki da dama game da rayuwar al’umma da kishin kasa, kuma shugaban kasar Sin, babban sakataren kolin JKS, kana shugaban hukumar gudanarwar rundunar sojojin kasar Xi Jinping, ya kan tsamo wasu kalmomin dake wakokin Qu Yuan, yayin da yake jawabi. Misali ya taba cewa: Kaunar kasar mu, da daura niyyar bautawa kasa, da kewar kasar mu ta haihuwa, nauyi ne dake wuyan dukkanin al’ummar Sinawa. Tarihin kasar Sin ya shafe dubban shekaru, kuma kishin kasa ya jima da zama jigo, kuma wani irin karfi dake ingiza dukkanin kabilun kasar Sin wajen cimma manyan nasarori.

Yayin da ake tunkarar rayuwa ta gaba, dole ne Sinawa su yayata kishin kasa, da martaba kimar kasa, da samun karfin gwawi tsakanin jama’a, da karfafa manufar “zama tsintsiya madaurinki daya”.  (Saminu)