logo

HAUSA

Najeriya ta amince da shirin aikin shimfida bututun iskar gas zuwa Morocco

2022-06-02 09:50:22 CMG Hausa

Gwamnatin Najeriya jiya Laraba, ta sanar da amincewa da wani shirin gina bututun iskar gas da zai hada Najeriyar da kasar Morocco.

Majalisar zartaswar kasar ce, a yayin taronta na mako-mako ta amince da kudirin da ma'aikatar albarkatun man fetur din kasar ta gabatar, inda ta umurci hukumar kula da albarkatun man fetur ta kasa (NNPC), da ta aiwatar da yarjejeniyar fahimtar juna da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) kan aikin, kamar yadda Timipre Sylva, karamin ministan albarkatun man fetur, ya sanar a wani taron manema labarai a Abuja, fadar mulkin Najeriya.

Kafofin yada labaran kasar sun bayyana cewa, shirin zai kasance daya daga cikin bututan mai a teku mafi tsayi a duniya, wanda zai kai tsawon kimanin kilomita 7,000.

Sylva ya ce, ana sa ran bututun iskar gas din, zai rika jigilar wani adadi na iskar gas zuwa kasashen yammacin Afirka da Morocco, da kuma ta Morocco zuwa Sifaniya da sauran kasashen Turai.

Najeriya, wadda Allah ya albarkace ta yawan iskar gas musamman a cikin ruwa mai zurfi, tana daya daga cikin kasa mai yawan ma'adinan iskar gas a Afirka. (Ibrahim)