logo

HAUSA

Kafar yada labarai: Masu neman ’yancin mallakar bindiga a Amurka na da matukar karfi yayin da ’yan siyasar kasar ke da rauni

2022-06-02 12:57:23 CMG Hausa

Mujallar kiwon lafiya ta Birtaniya (BMJ), ta bayyana cikin wani sharhi dake cewa, masu rajin ’yancin mallakar bindiga a kasar Amurka suna da matukar karfi, yayin da ’yan siyasar kasar ke da rauni matuka.

A rahoton da mujallar BMJ ta wallafa a ranar Laraba ya bayyana cewa, bayan kowane harbe-harben kan mai uwa da wabi da aka samu a makarantu, ana shiga cikin yanayin damuwa matuka a duk fadin kasar, tare da ziyarar shugaban kasar zuwa birnin ko garin da lamarin ya afku, sannan da yin alkawurran samar da sabbin dokokin da za su hana sake faruwar harbe-harben bindigar a makarantun kasar a nan gaba. Amma babu abin da ya sauya, har zuwa lokacin da za a sake samun wani maharin da ya kashe rayukan a karo na gaba.

Abin bakin ciki shi ne, kwana guda bayan harbe-harben bindiga mafi muni da aka kaddamar kan wata makarantar firamare a garin Uvalde, na jahar Texas, sai ga shi an samu tashin farashin muhimman kayayyaki masu alaka da bindigogi.

Greg Abbott, gwamnan jahar Texas, ya jaddada cewa, yana yin aiki tukuru wajen daidaita matsalar, ta hanyar tsaurara matakan yaki da wannan barazana da makarantun ke fuskanta, tare kuma da inganta tsarin kula da mutanen dake da matsalar tabin hankali.

Sai dai kuma, ya yi ikirarin cewa, bindigogi ba su ne matsalar ba.

An samu harbe-harben kan mai uwa da wabi sau 213 a makonni 21 na farkon shekarar 2022 a Amurka, wanda ya hada da harbe-harbe 27 da aka kai a makarantu, sai wasu harbe-harben kusan guda 10 da ake samu a kowane mako, kamar yadda mujallar The New Republic ta wallafa a rahotonta na ranar Asabar game da tarihin hare-heren bindiga.

Jason Linkins, mataimakin editan mujallar, ya bayyana cikin rahoton da aka wallafa cewa, “wannan shi ne hakikanin halin da ake ciki a Amurka, wannan shi ne gaskiyar abin da ke faruwa, sabanin sauran sassan duniya, ana kara samun saurin yaduwar bindigogi a kasar Amurka.” (Ahmad)