logo

HAUSA

Wang Yi: Sin tana hulda da kasashe masu tasowa bisa gaskiya da adalci

2022-06-02 14:13:12 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar, Wang Yi ya ce, sabanin wasu manyan kasashen duniya, kasar Sin a ko da yaushe tana nacewa kan manufofin tabbatar da daidaito a tsakanin kasashe a tsarin diflomasiyyarta da kasashen duniya, kana tana yin hulda da dukkan kasashe masu tasowa, musamman kanana da matsakaitan kasashe, bisa gaskiya da adalci.

Wang ya yi wannan tsokaci ne a yayin tattaunawa da shugaban kasar Vanuatu, Tallis Obed Moses, a birnin Port Vila, fadar mulkin kasar Vanuatu.

Vanuatu, shi ne waje na shida da mista Wang ya ziyarta a rangadin aikinsa na tsawon kwanaki 10 a yankin Pacific, gabanin hakan, ministan harkokin wajen na Sin ya ziyarci tsibirran Solomon Islands, da Kiribati, da Samoa, da Fiji da kuma Tonga.

Ya ce kasar Sin za ta ci gaba da yin aiki tare da goyon bayan sauran kasashe masu tasowa, domin kare muradu da manufofi karkashin kundin mulki na MDD, wanda ya shafi kaucewa tsoma baki a harkokin cikin gidan sauran kasashe, da tabbatar da kiyaye adalci a tsarin cudanyar kasa da kasa. (Ahmad)