logo

HAUSA

Mutum 4 sun mutu, 41 sun samu raunuka a girgizar kasa a lardin Sichuan

2022-06-02 15:37:48 CMG Hausa

Ana ci gaba da gudanar da aikin ceto bayan mutuwar mutane hudu da wasu mutanen 41 da suka samu raunuka sakamakon girgizar kasa da ta afkawa birnin Ya'an na lardin Sichuan dake kudu maso yammacin kasar Sin a ranar Laraba, kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana a taron manema labarai da aka gudanar a safiyar yau Alhamis.

An samu hasarar rayuka da jikkatar mutanen ne a yankunan Lushan da Baoxing.

Sama da tawagar jami’ai 800 aka tura zuwa birnin Ya'an domin gudanar da aikin ceto, da kula da lafiyar mutanen da suka samu raunuka, da kwashe buraguzai a kan hanyoyi, da kuma kwashe mutanen da girgizar kasar ta shafa, kamar yadda hukumomin yankin suka bayyana.

Jimillar mutane 13,081 ne bala’in girgizar kasar ta shafa a birnin, yayin da gidaje 135 sun yi mummunar lalacewa, sai kuma wasu gidajen 4,374 da suka lalace amma ba mai tsanani ba. (Ahmad)