logo

HAUSA

Sin na adawa da yadda Amurka da New Zealand ke tsoma baki a harkokin cikin gidanta

2022-06-01 20:37:00 CMG Hausa

 

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian ya bayyana yau Laraba cewar, sanarwar hadin gwiwar da kasashen Amurka da New Zealand suka bayar ta gurbata ayyukan hadin kan Sin da kasashe tsibiran tekun Fasifik, da kara wa batun tekun kudu na kasar Sin gishiri, da furta kalaman da ba su dace ba a kan batutuwan Taiwan da Xinjiang da Hong Kong da dai sauransu. Don haka kasar Sin ta nuna rashin amincewarta matuka, saboda hakan tamkar tsoma baki ne a harkokin cikin gida na kasar Sin karara.

Zhao ya ce, Sin da kasashe tsibiran tekun Fasifik za su ci gaba da mara wa juna baya, da taimaka wa juna, da kiyaye babbar moriyar juna da muhimman batutuwan da suke mai da hankali a kai, a kokarin inganta dangantakar abota a tsakaninsu daga dukkan fannoni bisa manyan tsare-tsare.

Zhao ya kuma kara da cewa, batutuwan Taiwan da Xinjiang da Hong Kong, harkokin cikin gidan kasar Sin ne, kuma ba za ta yarda ko kadan wasu kasashen waje su tsoma baki a ciki ba.(Kande Gao)