logo

HAUSA

Xi ya mika sakon taya murna ga sabon shugaban kasar Somaliya

2022-06-01 13:51:27 CMG Hausa

Kwanan baya, shugaban kasar Sin ya buga waya ga takwaransa na kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud, domin taya shi murnar sake lashe babban zaben shugaban kasar Somaliya.

Xi Jinping ya ce, kasar Sin da kasar Somaliya suna da zumunci mai zurfi, a koda yaushe, suna nuna goyon baya ga junansu kan manyan batutuwan dake shafar moriyarsu. Kasar Sin tana mai da hankali matuka wajen raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Kuma, shugaba Xi yana fatan yin hadin gwiwa da shugaba Mohamud domin zurfafa huldar dake tsakanin kasashen biyu a fannoni da dama, ta yadda za a tallafawa jama’ar kasashen biyu kamar yadda ake fata. (Maryam)