logo

HAUSA

Ana ci gaba da kyautata tsarin cinikayya da kasashen waje a Sin

2022-06-01 12:11:54 CMG Hausa

Cikin shekaru 10 da suka gabata, kasar Sin ta sami gaggarumin ci gaba a fannin cinikayya da kasashen waje, inda tsarin cinikayya da kasashen waje na kasar ke ci gaba da kyautatuwa. A shekarar 2021, adadin cinikayya da sabbin kasuwanni ya karu da kashi 6.2 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2012, yayin da adadin cinikayya da tsakiyar yankuna da yammacin yankunan kasar, ya karu da kashi 5.9 bisa dari. Haka kuma, adadin cinikayya da kamfanoni masu zaman kansu suka yi ya karu da kashi 20.1 bisa dari. Kana, adadin cinikayyar da aka saba yi, ya karu da kashi 12.7 bisa dari. Har ila yau, yawan hajojin da aka fitar da shigar yankunan tsakiya da yammacin kasar ya karu matuka. Kuma, bunkasuwar kamfanoni masu zaman kansu ta taimaka matuka wajen kyautata fasahohin dake shafar motoci da jiragen ruwa da sauransu. Lamarin da ya sa, adadin motocin da aka fitar zuwa kasashen waje ya karu da kashi 150 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2012. A sa’i daya kuma, cinikayyar hidimar fasaha ta karu da kashi 122.1 bisa dari, idan aka kwatanta da na shekarar 2012.

Bugu da kari, kyautatuwar da tsarin cinikayya da kasashen ketare yake ci gaba da yi, ya taimaka wajen kafa shirye-shiryen hadin gwiwa sama da guda 100 a fannonin zirga-zirga, zuba jari, cinikayyar ba da hidima da kuma harkokin kasuwanci ta yanar gizo a nan kasar Sin. Ban da haka kuma, manyan bukukuwan baje kolin da aka cimma nasarar gudanarwa a kasar Sin, sun ba da muhimmiyar gudummawa wajen raya cinikayya da kasashen ketare. Misali, jimillar cinikayyar da aka kulla yayin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su Sin na CIIE da aka yi a birnin Shanghai, ta kai dallar Amurka biliyan 272.27, inda aka shigo da kayayyaki masu inganci da fasahohi masu kyau da yawa. (Mai Fassara: Maryam Yang)