logo

HAUSA

Sin ta bukaci hadin gwiwar bangarori daban-daban don hana yaduwar makaman nukiliya

2022-06-01 10:50:14 CMG Hausa

Zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Zhang Jun ya ce, hana yaduwar makaman nukiliya wani babban kalubale ne na kasa da kasa. Domin daidaita wannan batu, akwai bukatar a tabbatar da hakikanin hadin gwiwar bangarori daban-daban, kuma jagorancin MDD na da matukar muhimmanci game da wannan batu. Zhang Jun ya bayyana hakan ne a yayin bude taron tuntubar juna game da yin cikakken nazari domin aiwatar da kudurin kwamitin sulhun MDD mai lamba 1540, da farko wannan kuduri ya dora alhakin wajabtawa dukkan kasashe mambobin kwamitin sulhun MDD, da su yi kokarin dauka tare kuma da aiwatar da kwararan matakan yaki da bazuwar makamai a tsakanin al’umma wadanda ake amfani da su wajen tafka mummunar barna wato (WMDs), sannan a yi kokarin dakile hanyoyin da ake jigilarsu, da sauran kayayyakin da ake amfani da su wajen ta da rikici.

Game da wannan batu, ya bukaci a tabbatar da hadin gwiwar bangarori daban-daban a bisa gaskiya.

Da yake bayani game da yadda za a tabbatar da hadin gwiwar kasa da kasa don tinkarar batun hana bazuwar makamai a duniya, Zhang Jun ya bayyana cewa, hana yaduwar makaman nukiliya NPT shi ne kashin bayan shirin hana yaduwar makamai na kasa da kasa, kuma hakan wani muhimmin jigo ne wajen daidaita matsalar tsaron kasa da kasa daga barazanar barkewar yaki.

Jakadan ya kuma bukaci yin amfani da kimiyya da fasaha don tabbatar da zaman lafiya da kuma gudanar da hadin gwiwar kasa da kasa kan wannan batu, wanda ya kasance hakki ne na wajibi da ya rataya a wuyan kowace kasa bisa tsarin dokokin kasa da kasa. (Ahmad Fagam)