logo

HAUSA

Sabon nau’in Omicron shi ne ya mamaye kaso 60 na sabbin masu kamuwa da cutar COVID-19 a Amurka

2022-06-01 11:27:01 CMG Hausa

Jiya Talata, cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Amurka CDC, ta ce sabon nau’in kwayar cutar Omicron na COVID-19, shi ne ya mamaye kaso 60 na sabbin wadanda suka kamu da cutar a baya bayan nan a kasar.

Cibiyar ta ce sabon nau’in da ake kira da BA.2.12.1, na bazuwa cikin sauri fiye sauran nau’ikan Omicron da suka bullo a baya.

Ta kara da cewa, zuwa karshen watan Maris, kaso 3.4 na sabbin masu kamuwa da cutar kadai sabon nau’in ya dauka. Amma adadin ya karu zuwa kaso 31.8 a karshen watan Afrilu, sannan ya karu zuwa kaso 59.1 a karshen watan Mayu.

Sabon nau’in ya rikide ne daga nau’in BA.2, wanda ya fi saurin yaduwa akan dukkanin nau’ikan cutar COVID-19.

A cewar cibiyar ta CDC, a matsakaicin mataki, Amurka na samun sama da mutane 100,000 dake kamuwa da cutar a kowace rana. Masana kiwon lafiya sun yi hasashen samun karuwar sabbin wadanda za su kamu da cutar bayan tafiye-tafiye da taruka na hutun ranar tunawa da mazan jiya ta Memorial Day. (Fa’iza Mustapha)