logo

HAUSA

Xi Ya Aike Da Ta'aziyya Ga Takwaransa Na Brazil Kan Mummunar Ambaliyar Ruwar Da Ta Afkawa Kasar

2022-06-01 19:32:12 CMG HAUSA

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon ta'aziyya ga takwaransa na kasar Brazil Jair Bolsonaro, sakamakon mummunar ambaliyar ruwa da ta yi sanadin salwantar rayuka a kasar.

A cikin sakon nasa, shugaba Xi ya ce ya kadu matuka da samun labarin mummunar ambaliyar ruwar da ta afku a arewa maso gabashin Brazil, wadda ta haddasa hasarar rayuka da dukiya.

Shugaba Xi ya kuma mika sakon ta'aziyya da ma jajantawa iyalan wadanda suka rasa rayukansu, da jama'ar yankunan da bala'in ya shafa.

Ya kuma yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin hanzari.(Ibrahim)