A Kan Shirya Shagulgula Iri Iri Domin Murnar Ranar Yara ta Kasar Sin
2022-06-01 09:39:01 CMG Hausa
A kan yi bikin ranar yara a lokuta daban-daban a sassan daban-daban na duniya. Sai dai a nan kara Sin, a kan yi bikin wannan rana ce a ranar 1 ga watan Yunin kowace shekara a matsayin ranar yara ta kasa da kasa da ake bikin ta a fadin duniya.
Wannan rana dai samo asali ne tun a shekarar 1856. Lokacin da wani mutum mai suna Rev. Dr. Charles Leonard ya shirya taron addu'a na musamman don yara, ya kuma kira wannan rana da suna "Rose Day”. Daga bisani ya canja sunan zuwa "Flower Sunday”, har zuwa lokacin da aka mayar da wannan rana da sunan "Ranar Yara".
Wannan rana kamar sauran muhimman ranaku da ake bikinsu a duniya, rana ce ta murna da farin ciki da annashuwa, duba da yadda su ma Sinawa ke daukar yara a matsayin manyan gobe. Wannan ya sa Sinawa suka kuduri aniyar kara ba da gudummawa wajen ganin yara sun samu iyalai, ilimi da yanayin rayuwa mai inganci daga dukkan fannoni.
A wannan rana, ma'aikatar tsaron jama'a tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyi uku, su kan shirya wani babban taro, inda ake gayyatar yara sama da 100 dake wakiltar sassan kasar daban-daban kimanin hamsin da shida. Manufar ita ce baiwa yaran damar kulla dangantaka mai kyau tare da sanin juna, ta yadda hakan zai taimaka musu wajen yin aiki tare nan gaba don bunkasa kasa da kowa zai ji dadin zama a cikinta.
Wani abin murna da farin ciki shi ne, a wannan rana, dukkan wuraren shakatawa kamar Sinima da filayen shakatawa suna kasancewa kyauta ga yara, baya ga liyafa da kyaututtuka da taruka da jawabai da laccoci da shirye-shirye a gidajen rediyo da talabijin da ake shiryawa yaran albarkacin wannan rana. (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)