logo

HAUSA

Shugaba Xi Jinping ya zanta da takwaransa na Zambia

2022-05-31 20:19:27 CMG Hausa

A yau Talata ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya zanta ta wayar tarho da takwaransa na kasar Zambia Hakainde Hichilema. Yayin tattaunawar ta su, shugaba Xi ya ce cikin shekara guda, adadin cinikayyar dake tsakanin Sin da Zambia ya kai matsayin koli, kuma Zambia ta zama kasar Afirka mafi jawo jarin kai tsaye daga kasar Sin.

Shugaba Xi ya ce kasar sa na dora muhimmancin gaske, ga alakar ta da Zambia, tana kuma fatan Zambia za ta dinke, tare da kara zurfafa abota, da ingiza alakar dake tsakanin ta da Sin zuwa sabon matsayi, wanda zai game karin sassa masu fadi.

A nasa bangare kuwa, Mr. Hitchilema cewa ya yi, karkashin kyakkyawan jagorancin Shugaba Xi Jinping, Sinawa sun samu ci gaba da bunkasuwa, kuma kasar sa na matukar sha’awar nasarorin da Sin din ta samu. Daga nan sai ya sake godewa kasar Sin, bisa tsawon lokaci da ta shafe tana tallafawa shirin Zambia na samun ci gaba, baya ga tallafin alluran rigakafin annobar COVID-19 da Sin din ta tallafawa kasar da su.

Shugaban na Zambia ya kara da cewa, gwamnatin sa a shirye take da ta karfafa musaya da koyi da JKS, domin ingiza babban ci gaban alaka, da moriyar al’ummun kasashen biyu. (Saminu)