logo

HAUSA

Sin da kasashen tsibiran tekun Pacific sun yi taron ministocin harkokin waje karo na biyu

2022-05-31 13:31:05 CMG HAUSA

 

Jiya Litinin, mamban majalisar gudanarwar kasar Sin, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi  da firaminista kana ministan harkokin wajen kasar Fiji Voreqe Bainimarama suka jagoranci taron ministocin harkokin wajen Sin da kasashen tsibirin tekun Pacific karo na biyu a birnin Suva. Yayin taron, Wang ya ce, hadin kan Sin da wadannan kasashe, ya dace da halin da duniya ke ciki da amfanawa al’ummar yankin tare da samar da makoma mai haske da kwarin gwiwa da kyakkyawan fata. Wang ya sanar da cewa, Sin za ta ci gaba da kafa sabbin hanyoyin hadin gwiwa 6 don ingiza hadin kansu a fannoni kawar da talauci da sauyin yanayi da tinkarar bala’u da aikin gona da namon laimar kwado da sauransu. (Amina Xu)