logo

HAUSA

Wang Yi: Ci gaba da samun wadatar bai daya tsakanin Sin da kasashe masu tasowa za su wanzar da daidaito da walwala

2022-05-31 19:44:41 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya ce kasar Sin na matukar goyon baya, da tallafawa tsibiran tekun kudancin Pacific, saboda hakan nauyi ne a wuyan ta, a matsayin ta na kasa mai tasowa mai kima. Wang ya ce a can baya da ma yanzu, ba wai kasashen wannan yanki kadai Sin ke tallafawa ba, har ma da sauran kasashe masu tasowa dake nahiyar Afirka, da Asiya, da na Latin America da dai sauran su.

Wang Yi ya yi wannan tsokaci ne, bayan ya jagoranci taro karo na 2, na ministocin wajen kasar Sin da na tsibiran tekun kudancin Pacific a kasar Fiji.

A cewar Wang, ga misali tun farkon shekarun 1960, Sin ta zage damtse wajen gina layukan dogo a kasashen Afirka, kuma har kullum Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasashe masu tasowa, da sauran kasashe matsakaita da kanana.

Daga nan sai ya yi kira ga wasu sassa, da su kauracewa yawan nuna damuwa, duba da cewa, ci gaba, da wadata da Sin tare da wasu kasashe masu tasowa suka samu, zai amfani duniya ne baki daya, ta hanyar wanzar da daidaito da walwala.(Saminu Alhassan)