logo

HAUSA

Sin na gabatar da shirin ingiza amfani da makamashi na zamani yadda ya kamata

2022-05-31 12:03:18 CMG HAUSA

 

 Jiya ne, ofishin gudanar da ayyukan majalisar gudanarwar Sin ya ruwaito shirin da hukumar raya kasa da yin kwaskwarima da hukumar makamashi suka gabatar cikin hadin gwiwa, mai suna “Shirin ingiza amfani da makamashi na zamani mai inganci”, da zummar tabbatar da burin samar da wutar lantarki fiye da KW miliyan 1200 ta hanyar amfani da karfin iska da haske rana kafin shekarar 2030, ta yadda za a gaggauta kafa tsarin amfani da makamashi mai tsabta mai tsaro da inganci.

A cikin ‘yan shekarun nan, Sin ta samu ci gaba mai armashi a fannin samar da wutar lantarki ta hanyar amfani da makamashin iska da haske rana. An gabatar da wannan shiri ne a kan lokaci don ingiza samun bunkasuwa a wannan fanni, wanda ya kunshi manufofi 21 a fanonni 7.

Darektan sashen makamashi na zamani na hukumar makamashin Sin Li Chuangjun ya nuna cewa, mallakar dimbin kwal da karancin man fetur da gas, shi ne halin da Sin ke ciki, don haka kamata ya yi makamashi na zamani su maye gurbin wadannan makamashi bisa shirin da ake yi sannu a hankali, wannan shiri na da muhimmanci matuka, ya ce:

“Da farko, dole ne a tabbatar da samun isasshen makamashi na zamani, na biyu a yi amfani da su yadda ya kamata, na uku a yi amfani da fasahohi na zamani, don tabbatar da matsayin Sin na kasancewa a sahun gaba a cikin gida a fannin samar da wutar lantarki mai amfani da karfin iska da haske rana, har ma a fannin karfin takara a fadin duniya, hakan zai sa Sin za ta iya samun sabon ci gaba da dogaro da kai a wannan fanni.” (Amina Xu)