logo

HAUSA

Sin ta musunta kalaman Amurka na wai yadda Sin ta gindaya sharadi ga ziyarar babbar kwamishinar MDD a kasar Sin

2022-05-30 20:40:27 CMG Hausa

 

Game da tsokacin da kasar Amurka ta yi kan wai “yadda Sin ta gindaya sharadi ga ziyarar Verónica Michelle Bachelet Jeria, babbar kwamishiniyar MDD ta fanni kare hakkin bil Adama a kasar Sin”, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana a yau Litinin cewa, Madam Bachelet ta taba bayyanawa a gun taron manema labarai, cewar ta yi mu’amala sosai ba tare da an sanya mata ido ba, a yayin da take ziyara a Sin.

Madam Bachelet ta gudanar da dukkan harkokin aiki a yayin ziyarar ta bisa burinta, bayan da bangarorin biyu suka yi shawarwari sosai a kai.

Wadda ke son yin coge kan ziyarar ita ce Amurka. Alal hakika Amurka, ba ta kula da yanayin hakkin bil Adama ko kadan, abin da take son yi shi ne shafa wa kasar Sin bakin fanti, da hana ci gaban Sin bisa hujjar hakkin bil Adama. Tun tuni kowa ya riga ya gane wannan makarkashiya ta Amurka a siyasance. (Kande Gao)