logo

HAUSA

Sin: Amurka ita ce wadda ta fi kalubalantar tsarin duniya cikin dogon lokaci

2022-05-30 20:55:08 CMG Hausa

 

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya furta yau Litinin cewa, jawabin da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Antony Blinken ya yi kan manufofin kasar sa game da kasar Sin cike yake da karya, ya kuma mayar da fari baki. Zage-zagen da Amurka ta saba yi game da kasar Sin shi ne abubuwan da take yi a yanzu.

Zhao ya nuna cewa, Amurka ba ta mutunta kundin tsarin mulkin MDD, da tsarin duniya da aka kafa bisa tushen dokokin kasa da kasa ko kadan. Amurka ita ce wadda ta fi lalata tsarin duniya, ba ta cancanci tabo magana kan ka’idoji ba.

Haka kuma Zhao ya jaddada cewa, hakikanin abubuwa za su kara shaida cewa, ko da yaushe kasar Sin na dukufa wajen shimfida zaman lafiyar duniya, da bayar da gudummawa ga ci gaban duniya, da ma kiyaye tsarin duniya. (Kande Gao)