logo

HAUSA

Sin ta yi alkawarin raba sakamakon ci gaban da ta samu tare da kasashen tsibirin Pacific

2022-05-30 10:22:37 CMG Hausa

Mamban majalisar gudanarwar kasar Sin kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya bayyana a jiya Lahadi cewa, kasar Sin za ta kara fadada da zurfafa bude kofa ga kasashen waje, kuma tana son raba sakamakon ci gaban da ta samu da kasashen tsibirin Pacific.

Wang ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da Henry Puna, babban sakataren dandalin tattaunawar tsibiran Pacific, a Suva, babban birnin kasar Fiji.

Fiji ne zango na hudu, a rangadin aiki na kwanaki 10 da Wang Yi ke yi, bayan ziyarar da ya kai tsibirin Solomon, da Kiribati da Samoa. Jami'in diflomasiyyar na ziyarar aiki a kasar Fiji, inda kuma zai jagoranci taron ministocin harkokin wajen kasashen Sin da na tsibirin Pasifik karo na biyu.(Ibrahim)