logo

HAUSA

Kamfanoni Masu Jarin Waje Dake Kasar Sin Na Kara Fadada Harkokinsu In Ji Sakamakon Wani Bincike

2022-05-30 19:44:53 CMG HAUSA

Kamfanoni masu jarin waje dake hada-hada a cikin kasar Sin, na kara fadada harkokinsu, duba da irin kyakkyawan yanayi gudanawa da suke samu.

Sakamakon wani bincike na baya-bayan nan ya nuna cewa, irin wadannan kamfanoni sun gamsu, da muhallin gudanar da kasuwanci na kasar Sin, wanda hakan ya sa mafi yawansu ci gaba da aiki, wasu kuma na kara fadada hada-hada a rubu’in farko na bana.

Binciken wanda hukumar ingiza hada-hadar kasuwancin kasa da kasa ta kasar Sin ta gudanar, ya kuma bayyana cewa, kamfanoni masu jarin waje, na da kwarin gwiwar samun karin damammaki na bunkasa kasuwancinsu a Sin, da kuma daidaito a hasashen ci gaban su.

Hukumar ta kara da cewa, idan an kwatanta da rubu’i na 4 na shekarar 2021, kaso 71 bisa dari na kamfanonin dake da jarin waje sun tsaya matsayinsu na gudanar da harkoki, yayin da kaso 16.4 bisa dari kuma suka kara fadadawa. Kaza lika binciken ya nuna yadda kamfanonin dake da jarin waje ke ci gaba da nuna karfin gwiwa, game da ci gabansu a kasar Sin, inda cikinsu kaso 13.5 bisa dari ke da shirin kara yawan jarinsu a wannan kasa ta 2 mafi karfin tattalin arziki a duniya.  (Saminu)