logo

HAUSA

Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya Na Kasar Sin Kusan Dubu 50 Sun Shiga Ayyukan Kare Zaman Lafiya Na MDD

2022-05-29 16:21:01 CMG HAUSA

Ranar 29 ga watan Mayu, ranar ma’aikatan kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa ce karo na 20.

Alkaluman ma’aikatar tsaron kasar Sin sun nuna cewa, a cikin shekaru fiye da 30 da suka wuce, sojojin kasar Sin kusan dubu 50 sun shiga ayyuka guda 25 na MDD na kiyaye zaman lafiya baki daya. Kasar Sin ta dauki hakikanin matakai wajen kiyaye zaman lafiyar duniya, ta zama kasa ta farko wadda ta fi tura sojojin wanzar zaman lafiya, cikin kasashe 5 da ke da kujerun dindindin cikin kwamitin sulhu na MDD.

Cikin shekaru fiye da 30 da suka wuce, rundunar sojan kasar Sin ta tura yawan sojoji masu ayyuka daban daban, wadanda suka kiyaye zaman lafiya a kasashen Cambodia, Jamhuriyar Demokuradiyyar Kongo, Liberia, Sudan, Lebanon, Cyprus, Sudan ta Kudu, Mali, Afirka ta Tsakiya da sauran kasashe da yankuna 20, inda suka ba da muhimmiyar gudummowa wajen daidaita rikici cikin ruwan sanyi, da kiyaye tsaro da kwanciyar hankali a yankuna, da kara azama kan bunkasar tattalin arziki da zaman al’ummar kasashen.

Yayin da sojojin kasar Sin suke gudanar da ayyukan MDD na kiyaye zaman lafiya, har kullum suna mayar da hankali wajen “sauke nauyin dake bisa wuyansu, na kiyaye zaman lafiyar duniya, da raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan dan Adam” a matsayin burinsu da aikinsu, sun ba da muhimmin karfi wajen kare zaman lafiyar duniya, sun kuma zama ginshikan MDD na kiyaye zaman lafiya. (Tasallah Yuan)