logo

HAUSA

Shawarar BRI ta karawa ci gaban kasashen Afirka masu amfani da harshen Faransanci kuzari

2022-05-28 16:22:13 CMG Hausa

Masana a nahiyar Afrika, sun bayyana cewa, shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ta kasar Sin, tana gina wani budadden dandali na hadin gwiwa da karfafa ci gaban kasasen Afrika masu amfani da harshen Faransanci.

Masanan sun bayyana haka ne yayin da suke halartar taron karawa juna sani na yini 3 dake gudana a Yaounden Kamaru.

Taron wanda cibiyar dake sa ido kan huldar Sin da kasashen Afrika masu amfani da harshen Faransanci ta shirya kan tasirin shawarar Ziri Daya da Hanya Daya a wadancan kasashe, ya samu daruruwan mahalarta da suka hada da ‘yan siyasa da masana da wakilan kamfanonin kasar Sin da daliban jami’a.

Da yake jawabi, shugaban cibiyar Jimmy Yab, ya ce hadin gwiwar moriyar juna shi ne jigon shawarar.

A nasa bangaren, Ronie Bertrand Nguenkwe, masanin tattalin arziki da bincike, a jami’ar Yaounde ta II, ya ce gudunmuwar da shawarar ta bayar ta nuna a fili cewa, ta na mayar da hankali ne kan hadin gwiwa da musayar moriya da muradu na bai daya. (Fa’iza Mustapha)