logo

HAUSA

Xi: ya kamata a kara nazarin wayewar kan Sinawa da karfafa yakini kan al'adu

2022-05-28 15:39:13 CMG Hausa

 

Ofishin kula da harkokin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya gudanar da zama na 39 na nazari game da shirin binciken kasa, wanda ke mayar da hankali kan bibiyar asalin wayewar kan Sinawa.

Zaman da aka yi a jiya Juma'a, ya gudana ne karkashin shugaba Xi Jinping, kuma sakatare janar na kwamitin tsakiya na JKS, inda ya yi kira da a kara kokarin nazartar wayewar kan Sinawa tare da kara kwarin gwiwar al'umma kan al'adun kasar. (Fa’iza Mustapha)