logo

HAUSA

Rundunar sojin Sin ta kira taro kan yanayin tsaro a gabar tekun Guinea

2022-05-28 16:35:24 CMG Hausa

Shugaban sashen watsa labarai na ma’aikatar tsaron kasar Sin kuma kakakin ma’aikatar Wu Qian, ya ce rundunar sojin kasar Sin ta kira taron kara wa juna sani ta kafar bidiyo, kan yanayin tsaron gabar tekun Guinea, domin tabbatar da shawarar tsaron duniya da tunanin kafa kyakkyawar makoma a kan teku, da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar. Tare kuma da kara karfafa hadin gwiwar dake tsakanin rundunar sojin Sin da na kasashen dake gabar tekun Guinea, kan tabbatar da tsaro a kan teku.

Taken taron shi ne, “tabbatar da tsaro a gabar tekun Guinea, ta hanyar kafa kyakkyawar makoma a kan teku”.

Babban kwamishinan rundunar sojin ruwa ta kasar Sin, Dong Jun, ya halarci taron tare da gabatar da jawabi. Haka kuma, taron ya samu halartar shugabannin rundunar sojin ruwa da rundunar soji masu gadin gabar teku na kasashen dake yankin gabar tekun Guinea, da wasu shugabannin kungiyoyin shiyyar.

Mahalartan taron sun kuma tattauna kan batutuwan da suka shafi tsaron teku a gabar tekun Guinea da dauwamammen ci gaban tattalin arziki da ayyukan sojojin ruwa da matakan da ya kamata su dauka. (Jamila)