logo

HAUSA

Harin bindiga ne kan gaba wajen kisan yara a Amurka

2022-05-28 16:55:12 CMG Hausa

Cibiyar kandagarki da dakile yaduwar cututtuka ta Amurka, ta ce a shekarar 2020, wadda ita ce ta baya-bayan nan da aka samu alkaluman da aka tattara, harin bindiga da ya hada da kisan kai da kisan kai da kai, ya maye gurbin hatsari a mastsayin wanda ya fi sanadin mutuwar yara a Amurka.

Alakaluma sun nuna cewa, a shekarar 2020, jimilar yara 4,368 da suka hada da kanana da wadanda shekarunsu ba su kai 19 ba, sun mutu sanadiyyar harbin bindiga a Amurka. Adadin da ya karu da kaso 29.5 akan na shekarar 2019, kwatankwacin mutuwa 54 cikin yara miliyan 1, akan matsakaicin mataki. Har ila yau a shekarar, hadduran ababen hawa sun yi sanadin mutuwar yara 4,036 da suka hada da kananan yara da wadanda shekarunsu ba su kai 19 ba.

Daga shekarar 2020 zuwa shekaru 21 da suka wuce, hadduran ababen hawa ne jigo wajen kisan yara a Amurka, inda harin bindiga ke bi masa baya. Cibiyar na cewa, tun daga shekarar 2016 gibin dake tsakaninsu ya fara raguwa.

Alkaluma daga cibiyar sun nuna cewa, kusan daya bisa uku na harbe-harben, ana yin su ne da niyyar kisan kai, yayin da kaso 30 suka kasance na kisan kai da kai. A cewar cibiyar, yara Amurkawa bakaken fata, sun fi fuskantar barazanar mutuwa sanadiyyar harin bindaga fiye da takwarorinsu fararen fata, har sau 4. (Fa’iza Mustapha)