logo

HAUSA

An gudanar da taron ministocin ma’aikatun ilmi na kasashen BRICS karo na 9

2022-05-27 13:08:57 CMG Hausa

An gudanar da taron ministocin ma’aikatun ilmi na kasashen BRICS karo na 9 ta kafar bidiyo a jiya, wanda ma’aikatar harkokin bada ilmi ta kasar Sin ta karbi bakunci, inda aka zartas da sanarwar taron, da tabbatar da manyan ayyukan hadin gwiwa da za a gudanar a matakin nan gaba a fannin bada ilmi.

Mahalartar taron sun nuna godiya ga ma’aikatar harkokin bada ilmi ta kasar Sin bisa karbar bakuncin gudanar da taron, tare da nuna amincewa ga sakamakon da aka samu a yayin taron. 

Ministocin ma’aikatun ilmi na kasashen BRICS sun yi mu’amala da juna, da more fasahohinsu a gun taron, kana sun bayyana cewa, za su ci gaba da bin tunanin BRICS, wato bude kofa ga kasashen waje, da amince da bambance-bambance, da yin hadin gwiwa, da kuma samun nasara tare, da kara yin hadin gwiwa da juna a fannin bada ilmi, da tabbatar da nasarorin da aka samu kan hadin kai a fannin, da kara yin mu’amala da juna don tinkarar kalubale a fannin, da kuma sa kaimi ga bunkasa sha’anin bada ilmi na kasashen BRICS tare. (Zainab)