logo

HAUSA

Iraqi ta zartar da dokar haramta alaka da Isra’ila

2022-05-27 11:40:44 CMG Hausa

Majalisar dokokin Iraqi, ta amince da dokar da ta ayyana kyautata alaka da Isra’ila tsakanin hukumomi da jami’ai da daidaikun mutanen kasar a matsayin laifi.

Wata sanarwar da majalisar ta fitar, ta ce daukacin mambobi 275 da suka halarci zamanta na jiya ne suka amimce da dokar.

A cewar sanarwar, manufar dokar ita ce kare ka’idojin al’ummar Iraqi na kare Falasdinu da al’ummarta da ma al’ummar Larabawa, wadanda Isra’ila ta mamaye yankunansu.

Haka kuma, dokar na da nufin hana kullawa ko kyautata hulda da Isra’ila. (Fa’iza Mustapha)