logo

HAUSA

Sin na fatan karin kasashe za su shiga BRICS

2022-05-27 19:19:38 CMG Hausa

Yau Juma’a kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya yi tsokaci yayin taron ganawa da manema labaran da aka shirya cewa, a matsayinta na kasar dake shugabancin BRICS a bana, kasar Sin tana goyon bayan kasashen kungiyar, da su kara habaka mambobinsu, tare kuma da karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu da sauran kasashen duniya, tana kuma fatan karin kasashe wadanda ke da muradu iri daya za su shiga kungiyar ta BRICS.

A farkon bana, wasu kasashe kamar Argentina sun nuna fatansu na shiga BRICS, Wang Wenbin ya bayyana cewa, kungiyar BRICS, muhimmin tsarin gudanar da hadin gwiwa ne tsakanin kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki, haka kuma babban dandali ne na hadin gwiwar kasashe masu tasowa.

Tun bayan da aka kafa kungiyar shekaru 16 da suka gabata, ta samu ci gaba yadda ya kamata, kuma hadin gwiwar dake tsakanin kasashe mambobin kungiyar a fannoni daban daban yana kara karfafa, ana iya cewa, tun farkon kafuwarsa, tsarin hadin gwiwar dake tsakanin kasashe mambobin kungiyar BRICS yana taka babbar rawa kan bunkasuwar kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki da kuma kasashe masu tasowa. (Jamila)