logo

HAUSA

Li Keqiang ya jaddada bukatar aiwatar da hakikanin matakai na tabbatar samun yabanya mai armashi

2022-05-27 11:04:19 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Keqiang ya yi kira da a kara azama wajen tabbatar da samun yabanya mai tarin yawa, a kakar amfanin gona ta bana.

Li ya yi wannan kira ne a jiya Alhamis, yayin taron da aka shirya ta kafar bidiyo. Ya ce lokacin girbi na bazara, na da ma’anar gaske wajen tabbatar da nasarar burin kasar Sin, game da cimma mizanin hatsi da aka yi hasashen samu, da daidaita farashi, da kuma tsara matakan yaki da annobar COVID-19, da ma bunkasa tattalin arziki, da ci gaban zamantakewar al’umma.

Firaministan na Sin, ya kuma bukaci da a samar da kayayyakin amfanin gona, da tsare-tsaren hidimomi da ake bukata, ya kuma yi kira ga sassan gwamnatoci a dukkanin matakai, da kar su bata lokaci, ko barnata duk wata kwayar hatsi da aka samu. (Saminu)