logo

HAUSA

Sin: NATO ta lalata Turai

2022-05-26 20:12:30 CMG Hausa

A martanin kalaman da babban sakataren kungiyar tsaro ta NATO Jen Stoltenberg ya yi a baya-bayan nan na neman bata sunan kasar Sin, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yayin taron manema labaru na yau da kullum Alhamis din nan cewa, babban sakataren kungiyar NATO, ya dade yana yada zarge-zarge marasa tushe da ma neman bata sunan kasar Sin. Don haka, kasar Sin tana adawa da kakkausar murya kan wannan lamari. Ya ce, kungiyar NATO ta riga ta dagula nahiyar Turai, don haka ta daina yunkurin dagula nahiyar Asiya da ma duniya baki daya.

Wang Wenbin ya kara da cewa, kasar Sin tana goyon bayan ci gaba da shawarwarin zaman lafiya tsakanin kasashen Rasha da Ukraine, kana tana kira ga kungiyar EU da NATO, da su gudanar da sahihin shawarwari da kasar Rasha, ta yadda kaifin hankali da hangen nesa zai iya gyara duk wasu kura-kurai.(Ibrahim)