logo

HAUSA

Shugaban NDB: Sin tamkar wani mayen karfe ne wajen janyo hankalin masu zuba jari na duniya

2022-05-26 18:30:14 CMG Hausa

Marcos Troyjo, shugaban bankin sabon ci gaba wato NDB, ya ce kasar Sin kamar wata mayen karfe ne dake janyo masu zuba jari, da kuma kara samar da damammaki ga kasuwanni masu tasowa da kuma kasashe masu tasowa, ya bayyana hakan ne a taron dandalin tattalin arziki na duniya WEF na wannnan shekarar ta 2022 a Davos.

“Kasar Sin za ta cigaba da zama a matsayin wani babban wuri wajen zuba jarin ketare na kai tsaye nan da dogon lokaci mai zuwa, in ji Troyjo.

Taroyjo ya ce, yawan adadin tattalin arzikin kasar, da yadda tattalin arzikin ke da karfin jure wahalhalu, ya baiwa kasar damar zama wata cibiyar samar da kima ga hajoji. Ya kara da cewa, manufar kasar Sin game da dunkulewar tattalin arzikin duniya zai ci gaba da samar da muhimman damammaki ga masu ruwa da tsaki kan tattalin arzikin duniya. (Ahmad)