logo

HAUSA

WEF ya yabawa kwazon kasar Sin a fannin yaki da annobar COVID-19

2022-05-26 18:17:40 CMG Hausa

Shugaban gangamin tsara matakan kyautata kiwon lafiya a nan gaba, karkashin dandalin raya tattalin arzikin duniya WEF Mr. Shyam Bishen, ya yi maraba da kiran da kasar Sin ta yi, game da gina tsarin kiwon lafiyar al’ummar duniya na bai daya, a gabar da duniya ke fuskantar kalubalen lafiya da annobar COVID-19 ta haifar.

Shyam, wanda ya yi tsokacin a lokacin ganawa da ‘yan jaridu, a gefen taron shekara shekara na WEF a jiya Laraba, ya ce dandalin ya jinjinawa gwazon gwamnatin kasar Sin karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, a fannonin samar da kudade, da dukkanin albarkatun da ake bukata na yaki da cutar COVID-19. (Saminu)