logo

HAUSA

Kasashe mambobin BRICS sun kaddamar da kwamitin hadin gwiwa game da binciken samaniya

2022-05-26 13:18:58 CMG Hausa

A jiya Laraba ne kasashe 5 mambobin kungiyar BRICS, suka kaddamar da wani sabon kwamitin hadin gwiwa, wanda zai bude sabon babi ga ayyukan su na amfani da taurarin dan adam, da musayar bayanai game da sararin samaniya tsakanin su.

Da yake tsokaci game da hakan ta kafar bidiyo, shugaban hukumar lura da ayyukan binciken sararin samaniya na kasar Sin Zhang Kejian, ya ce kwamitin zai tsara ayyukan hadin gwiwa tsakanin kasashen na BRICS, ta yadda za su ci gajiya daga managartan hidimomin sanya ido ta amfani da taurarin dan adam, matakin da zai taimaka wajen raya tattalin arziki da zamantakewar su.

Zhangya kara da cewa, sabon kwamitin zaibaiwa hukumomin binciken sararin samaniya na kasashe mambobinBRICS,damar aiki kafada da kafada, a fannoninkare muhalli,da kandagarkin bala'u daga indallahi, da shawo kan kalubalen sauyin yanayi, ta amfani da managarcin tsarin musayar bayanai.  (Saminu)