logo

HAUSA

Li Keqiang ya jaddada bukatar aiwatar da manufofin daidaita tattalin arzikin kasar Sin

2022-05-26 11:21:25 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada bukatar aiwatar da manufofin kasa, na daidaita ci gaban tattalin arziki, da tallafawa sassan kasuwanni, da bunkasa samar da ayyukan yi, da inganta rayuwar al’umma.

Li, wanda kuma mamba ne a ofishin siyasa na kwamitin kolin JKS, ya yi wannan tsokaci ne a jiya Laraba, yayin taron majalissar gudanarwar kasar Sin da ya gudana ta kafar bidiyo. Yana mai jan hankali da a kara azama wajen ingiza harkokin tattalin arziki bakin gwargwado.

Firaministan ya kara da cewa, ana aiwatar da matakai daban daban domin shawo kan wahalhalu, da kalubaloli da suka biyo bayan wasu al’amura da suka auku a bana.

Ya ce an fuskanci wahalhalu a watan Maris da ma watan Afirilu, wadanda kusan ta wasu fannonin sun dara na shekarar 2020, lokacin da annobar COVID-19 ta fara bulla a kasar, lamarin da ya haifar da koma baya a fannonin samar da guraben ayyukan yi, da sarrafa kayayyaki a masana’antu, da sashen amfani da makamashi, da safarar manyan hajoji ta ruwa, da dai sauran su.

Sai dai duk da haka, firaminista Li ya jaddada muhimmancin aiwatar da matakan ingiza ci gaba, wanda ya ce shi ne jigon warware duk wasu matsalolin kasar Sin, yana mai kira da tun daga yanzu, a gaggauta aiwatar da matakan dawo da tattalin arzikin kasar kan turba ta gari.

Ya kuma umarci da a aiwatar da cikakkun matakai, na ingiza salon ci gaban kasar Sin, a kuma tsara matakan shawo kan annobar COVID-19, hade da dabarun bunkasa tattalin arziki da zamantakewar al’umma bisa inganci, kana a daidaita ci gaba bisa kyakkyawan matsayi. (Saminu)