logo

HAUSA

Wakilin Sin: Yin amfani da “ma'auni biyu” na kawo babbar illa ga kare fararen hula

2022-05-26 15:11:07 CMG Hausa

Jiya Laraba, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar da da taro a fili kan batun “kare fararen hula a yayin rikici”. Game da hakan, mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya bayyana cewa, ya kamata kasashen duniya su ci gaba da yin kokarin kare fararen hula, da yin watsi da daukar “ma’auni biyu” kan batun.

A tsokacinsa, mukaddashin mataimakin Sakatare-Janar na Majalisar Dinkin Duniya mai kula da harkokin jin kai Ramesh Rajasingham, ya bayyana a sanarwar da aka bayar a yayin taron cewa, hatsarin asarar rayukan fararen hula na karuwa sosai, a rikicin da ake yi a yankunan da ke da yawan jama'a. Ya kuma yi kira ga dukkan bangarorin da su mutunta dokar jin kai, da kuma kauracewa amfani da makamai masu fashewa, da ke da tasiri sosai a wadannan yankunan.

Game da hakan, Dai Bing ya ce kasarsa ta gabatar da wasu abubuwa guda hudu, wadanda suka hada da mutunta dokar kasa da kasa, da ka’idojin kasa da kasa, da nacewa ga bin jagorancin kasashe mambobin kungiyar, da warware takaddama cikin lumana, da kuma neman ci gaba.

Ya ce kasar Sin ta jaddada cewa, yin amfani da “ma'auni biyu” na iya kawo babbar illa ga kare fararen hula. Kuma bai kamata a nuna bambanci a yayin da ake kare fararen hula ba, musamman ma wadancan kasashen da suka fi yawan tayar da yake-yake a kasashen waje cikin tsawon lokaci, kamata ya yi su tuba sosai daga aikata hakan. (Mai fassara: Bilkisu)