logo

HAUSA

Wang Yi ya bukaci a samar da damar fitar da hatsi daga rumbunan Ukraine

2022-05-25 16:16:05 CMG Hausa

Babban dan majalissar gudanarwa kuma ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi, ya yi kira ga sassan kasa da kasa da su sanya baki, wajen tabbatar da tsagaita bude wuta a Ukraine, tare da samar da damar fitar da hatsin kasar zuwa sassan dake bukata.

Wang Yi wanda ya yi kiran a jita Talata, yayin da yake zantawa da ministan harkokin wajen kasar Jamus Annalena Baerbock ta kafar bidiyo, ya ce Sin a shirye take ta yi hadin gwiwa da dukkanin sassa masu ruwa da tsaki, domin cimma nasarar dakile kalubalen karancin abinci da ake fuskanta, kuma Sin din ta jima tana bayar da tallafin gaggauwa na cimaka, ga kasashen dake cikin yanayi na tsananin bukata. (Saminu)