logo

HAUSA

Har yanzu Amurkawa bakaken fata ba su iya yin numfashi ba

2022-05-25 16:29:27 CMG Hausa

Mutuwar George Floyd, baAmurke bakar fata, a hannu dan sanda farar fata, wani babi ne na abun kunya a tarihin kare hakkin dan Adam na Amurka. Yayin da ake cika shekaru biyu da mutuwar Floyd, sanaddiyar danne masa wuya da gwiwa da dan sanda ya yi, kusan kowanne bangare na rayuwar al’umma a Amurka, ya fuskanci wannan mummunar cuta ta wariyar launin fata da cin zarafi daga jami’an tsaro.

Ra’ayoyin Amurkawa sun nuna cewa, duk da cewa mutuwar George Floyd ta yi gagarumin tasiri a cikin al’ummar kasar, matsalar wariyar launin fata a kasar, abu ne da zai yi wuya a shawo kansa. Kawo yanzu, babu wata kyautatuwa da yanayin Amurkawa bakaken fata ya samu a kasar.

Bisa alkaluman da shafin yanar gizo na “Police Violence Map”, mai bibiyar kisan da ‘yan sanda ke yi a Amurka ya samar, Amurkawa bakaken fata ne suka dauki kaso 20 na mutanen da suka mutu a hannu ‘yan sandan a shekarar 2021, yayin da kaso 13 kadai suka dauka cikin jimilar al’ummar Amurkar. (Fa’iza Mustapha)