logo

HAUSA

Dakarun PLA na gudanar da atisayen daura damara a kewayen tsibirin Taiwan

2022-05-25 16:51:38 CMG Hausa

Rundunar sojojin ‘yantar da al’umma da kasar Sin wato PLA, dake yankin gabashin kasar, ta kaddamar da ayyukan daura damara don zama cikin shirin ko-ta-kwana, a sashen ruwa da na sama, a yankunan kewayen tsibirin Taiwan, a matsayin wani gargadi game da goyon bayan da Amurka take ikirarin bayarwa a baya bayan nan ga dakarun “yancin Taiwan”, wani babban jami’in soji Kanal Shi Yi, kana kakakin rundunar PLA dake gabashi, ya bayyana hakan a yau Laraba.

Kakakin ya ce, Taiwan, wani bangare ne na kasar Sin, kuma rundunar PLA dake gabashi a shirye take ta tabbatar da tsaron yankunan da ikon yankunan, da kuma tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyyar. (Ahmad)